Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIndependence:Yajin aikin ASUU na sosamin rai-Buhari

Independence:Yajin aikin ASUU na sosamin rai-Buhari

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki malaman jami’oi da su janye yajin aikin da suka kwashe watanni su na yi.

 

Buhari ya yi wannan rokon ne yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar nan a wani bangare na zagayowar ranar samun ‘yancin kan kasar nan daga turawan mulkin mallaka.

 

ya ce halin da ’yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki yana ba shi tausayi.

 

“Na damu matuka kan tsaikon da aka samu a bangaren ilimin musamman rufe manyan makarantu.

 

“Ina rokon malaman jami’o’in su koma bakin aiki, sannan su ci gaba da tattaunawa domin daidaita al’amura.”

 

Haka kuma shuganan kasar ya roki ’yan siyasa da jam’iyyu da su guji duk wani abu da zai kawo matsala ga zaben 2023, domin a mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin kwanciyar hankali.

 

Ya kuma yi kira ga mata da matasa da su shiga a dama da su sosai a zaben da ke tafe.

 

“Ina fata matasanmu sun fahimci cewa tashin hankali babu abin da yake kawowa sai matsala ga zabe.

 

“Ina fata ba za su bari a yi amfani da su a wurin bangar siyasa ba a nan gaba,” in ji shi.

 

Buhari ya fara jawabin ne da godiya ga ’yan Najeriya bisa hakurin da suka yi da kamun ludayin gwamnatinnsa a tsawon lokaci.

 

“Kun yi hakuri da yunkurinmu da kura-kuranmu da kuma nasarorin da muka samu,” in ji shi.

 

Ya bayyana cewa duk da matsalolin da suka yi wa Najeriya tarnaki, gwamantinsa ta samun nasara a bangarori da dama, duk da cewa haka ba ta gama cim-ma ruwa ba.

 

“Daya daga cikin bangarorin da muka yi nasara shi ne bangaren yaki da almundahana da ta yi katutu a Najeriya.

 

“Mun karfafa hukumomin yaki da rashawa wanda ya kai ga tsare manyan masu laifi da kuma dawo da makudan kudade da aka sace mana aka kai aka boye a kasashen waje.”

 

Ya ci gaba da cewa a bangaren tsaro, “Mun yi aiki haikan domin dankwafe ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, muna kuma kokarin gamawa da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.”

 

Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin fita sau biyu daga matsin tattalin arziki.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...