Elizabeth II ta rasu ne a Balmoral Castle tana da shekara 96 a duniya.

 

Takardar shaidar rasuwarta ta nuna cewa marigayiyar ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:10 na yamma ranar 8 ga Satumba a Balmoral Castle dake Ballater.

 

Mutuwar Sarauniyar ta kawo ƙarshen mulkinta na shekara 70.

 

Ta ɗare karagar mulki ne ranar 6 ga Fabrairu, 1952, bayan rasuwar mahaifinta, Sarki George VI.

 

An haifi Elizabeth II ranar 21 ga Afrilu, 1926 a lokacin mulkin kakanta na ɓangaren uba, Sarki George V.

 

Elizabeth II ta kasance basarakiya mafi daɗewa akan mulki a tarihin Birtaniya.