33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar  ASUU kishiya

Gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar  ASUU kishiya

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Chris Ngige ya bayar da takardar shaida ga kungiyar ma’aikatan koyarwa ta jami’o’in kasar nan, wadda kungiya ce ta malaman jami’o’in tarayya da na jihohi.

Kungiyar mai suna CONUA  ana ganin kai tsaye za ta kasance kishiya ga babbar kungiyar malaman jami’ioin gwamnatin kasar nan.

Andai  kafa kungiyar CONUA ne a shekara ta 2018 a jami’ar jihar Osun.

 

Kungiyar ASUU da gwamnatin kasar nan na kai ruwa rana a dalilin  yajin aikin sai-baba-ta-gani da malaman jami’o’in suka shiga tsawon wata takwas ke nan, suna neman sai lallai gwamnati ta biya musu bukatunsu.

 

Duk da wani kokari da ban-baki da tattaunawa daga gwamnati sun kasa shawo kan kungiyar malaman kungiyar ASUU domin dakatar da yajin aiki.

Latest stories