Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Sunday, April 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari  ya zargi  ASUU da cin hanci da rashawa

Buhari  ya zargi  ASUU da cin hanci da rashawa

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cewa cin hanci da rashawa  da ake aitaikatawa  a jami’o’in kasar nan ya kai wani mizani da ba’a taba tsammani ba.

Zargin nasa na zuwa ne a yayin da kungiyar ta shafe wata bakwai tana yajin aiki, wanda ta fara tun ranar 14 ga watan Fabrairu.

Buhari ya bayyan hakan ne a wani  jawabi da yayi a wani babban taro kan hanyoyin rage cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati a kasar nan, inda yace  yana sane da irin cin hanci da rashawa dake gudana a jami’o’i, wanda wasu daga cikin malamai da dalibai ke aikatawa.

Ya kuma kara da cewa”daliabai na amfani da kudi  don sayen maki ko kuma yin lalata dasu don a gyara makin da kuma satar amsa a lokacin jarrabawa da sauransu.”

Buhari ya nunar da  cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC tana gudanar da bincike tare da gurfanar da mutanen da aka zarga da aikata lalata a a gaban koto a matsayin wani nau’in tozarta mukami a makarantun gwamnati.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories