Aminu Abdullahi
Majalisar dokokin Kano, ta amince wa gwamna Ganduje ya gabatar mata da ƙunshin Kasafin kuɗin shekarar 2023 a ranar Juma’a.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan da shugaban masu rinjaye Labaran Abdul Madari, ya sanar da mambobin zauren majalisar yayin zaman ta na ranar Laraba.
Bayan gabatar da buƙatar ne mambobin suka amince da buƙatar gwamnan.
