Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta umarci 'yan sanda su binciki Alhassan Ado Doguwa

Kotu a Kano ta umarci ‘yan sanda su binciki Alhassan Ado Doguwa

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kotun Magistrate a Kano ta umarci mataimakin sifeton ‘yan sanda na kasa da ke Kano(Zone 1) da ya binciki dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada Alhassan Ado Doguwa.

 

Wannan na cikin takardar umarni da aka aikewa mataimakin babban sifeton ‘yan sandan da ke dauke da kwanan watan 1 ga Nuwambar wannan shekara.

 

Cikin takardar wadda magatakardar kotun mai lamba 24 da ke zamanta a Gyadi-Gyadi ya sanyawa hannu, ta umarci lallai abinciki wanda ake zargin.

 

Wannan na zuwa ne bayan da wasu mutane suka shigar da korafi kan Doguwan na cin zarafin al’umma.

 

Idan za a iya tunawa a ranar Lahadin da ta gabata ne aka yada labarin an dambata tsakanin Alhassan Ado Doguwan da Kuma Murtala Sule Garo.

 

Murtala Garo ya dai zargi Doguwan da kwada masa Kofi tare da make wasu da suke gefensa.

 

Sai dai a taron manema labarai da Doguwan ya gudanar ranar Talata ya musanta dukkan zargin.

 

Inda ya ce Murtala Sule Garon ne ya ci zarafinsa ta hanyar zaginsa.

Ko a yau Laraba sai da wakilin jaridar Leadership a Kano ya shigar da Kara kotu kan zargin Doguwan ya mangareshi lokacin da ake waccan takaddama.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...