Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniAl'ummar Musulmi sunyi zanga-zanga a Mali

Al’ummar Musulmi sunyi zanga-zanga a Mali

Date:

Dubun dubatar mutane a birnin Bamako na kasar Mali sun yi zanga-zangar nuna adawa da batanci ga musulunci a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

 

Tuni dai hukumomi suka kama mutane shida da ake zargi da yada bidiyon wanda a cikinsa ake kalamai marasa dadi ga Musulmi da Musulunci.

 

Kaso 95 cikin 100 na mutanen kasar Mali dai Musulmai ne wadanda ba su amince da duk wani cin zarafi ga addininsu ba.

 

Sabanin wasu kasashen Yammacin duniya, a wannan kasa da ke Yammacin Afirka, dokokin kasar ba su bai wa masu yin batanci ga addini wata kariya ba.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories