Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMutum 18 sun rasu bayan harin Yan bindiga a Benue

Mutum 18 sun rasu bayan harin Yan bindiga a Benue

Date:

Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Ukohol dake karamar hukumar Guma da ke Jihar Benue.

 

Rahotanni sun bayyana cewa mai baiwa shugaban karamar hukumar shawara kan harkar tsaro Christopher Waku na cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin Alhamis lokacin da mutane suke tsaka da cin kasuwa a yankin.

 

Ya kuma ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka bata yayin harin.

 

Shi ma shugaban karamar hukumar, Mike Ubah, ya tabattar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun je wurin ne sanye da bakaken kaya, kuma da isarsu suka bude wa mutane wuta a cikin kasuwar, inda nan take mutum 10 suka mutu.

 

Ubah ya kara da cewa bayan haka sun kai hare-hare a kauyuka da ke kusa tare da kashe mutum takwas.

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan Benue, SP Catherine Anene, ta tabbatar da kai harin amma ta ce ba su da wani karin bayani ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...