Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaCutar Bakon Dauro ta bulla a Jihar Neja

Cutar Bakon Dauro ta bulla a Jihar Neja

Date:

Hafsat Iliyasu Dambo

 

Hukumar lafiya ta ankarar da al’ummar Jihar Neja kan hadarin cutar bakon dauro da ke barazana da kananan yara akalla 1,146,572 ‘yan tsakanin watanni shida zuwa shekaru biyar da haihuwa.

 

Jami’in kula da annobar bakon dauro na hukumar lafiya, Hassan Musa Abari, ya bayyana amfanin gudunmawar kafofin yada labarai wajen wayar da kan al’umma na amfanin rigakafin.

 

Abari ya ce yekuwar na da matukar alfanu ganin yadda aka fara samun rahotannin bullar annobar wanda ya yi sanadin mutuwar yara sha takwas a jihar a halin yanzu, don haka dukkanin mazabu 275 da ke jihar za a gudanar da aikin rigakafi.

 

Hukumar UNICEF ta ce gwamnatin jiha ta ba ta umurnin fara aikin kashin farko daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 7 ga watan Nuwamba, yayin zango na biyu da ya kunshi sauran kananan hukumomi zai fara daga ranar 8 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan, wanda ya kunshi Agwara, Bargu da Edati, Magama da Kontagora, Mariga da Mashegu, Rafi, Mokwa, Rijau da Wushishi.

 

Sauran su ne Chanchaga, Bosso, Paiko da Lapai, Gurara, Suleja, Labun, Munya, Shiroro da Katcha, Bida, Agaie da Gbako.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories