Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta sanar da ranar dawo da jigilar jirgin kasa na...

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar dawo da jigilar jirgin kasa na Kaduna-Abuja

Date:

Ministan sifuri na kasar nan Mu’azu Sambo ya ce Gwamnatin kasar nan ta shirya tsaf domin dawo da zirga zirgar jirgin kasan Kaduna Abuja a wannan  watan na nuwamban da muke ciki.

An dakatar da aikin jirgin kasan tun bayan wani harin bom da yan bindiga suka kai tare da sace wasu daga cikin fasinjojin  jirgin a ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata.

A kwanakin baya ministan yayi alkwari cewa baza’a dawo da aikin jirgin har se an sako fasinjojin da aka sace gaba daya.

Da yake sanar da dawowar ministan ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro a hanyar domin kaucewa faruwar irin wannan lamarin.

Ya kuma kara da cewa sun koyi darasi daga harin da aka kai inda ya bayyana cewa zasuyi kokarin ganin hakan bai kara faruwa ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...