Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn sanya ranar fara gasar Firimiyar Ingila ta kakar 2023/2024

An sanya ranar fara gasar Firimiyar Ingila ta kakar 2023/2024

Date:

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila, ta sanar da ranar fara sabuwar gasar Firimiya ta kakar wasannin 2023/2024.

 

Gasar wadda ake saran farawa a ranar Asabar 12 ga Agustan shekarar 2023 Mai zuwa.

 

Yayinda kuma ake saran kammala gasar, a ranar Lahadi 19 ga Mayun shekarar 2024 ba tare da bata lokaci.

 

Lamarin da ke nuna cewa gasar zata ci gaba da yadda tsarin ta yake a baya, sakamakon sauyin da aka samu biyo bayan bullar cutar COVID-19.

 

Haka zalika kwamitin da ke lura da shirya gasar, ya kuma bukaci kungiyoyi da su lura da wasannin lokacin Kirisimeti da na sabuwar shekara, wanda wasannin lokacin ba zasu gudana kasa da a wanni 48 ba.

 

Ana saran kuma wasannin tsakiyar kaka yan wasa zasu wuta, kana kuma a fafata wasannin a ranakun 13 da 20 ga watan Janairun shekarar.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...