Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiPDP ta zargi APC da kaiwa Atiku hari

PDP ta zargi APC da kaiwa Atiku hari

Date:

Jam’iyyar PDP ta zargi abokiyar hamayyar ta, APC da kaiwa dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar hari a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Mai magana da yawun kwamatin yakin neman zaben, Senator Dino Melaye ne yayi wannan zargi, yana mai cewa akalla mutum 70 sun jikkata.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga yadda mutane ke kokarin tserewa, yayin da ake harbi a sararin samaniya.

Gabanin harin dai, tawagar dan takarar ta isa jihar Borno, daya daga cikin jihohin da APC take mulki, domin gangamin yakin neman zabenta.

Rahotanni sun ce an ga hotunan motocin ayarin dan takarar da aka lalata a filin taro na Ramat da ke Maiduguri.
To sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, jam’iyyar ta APC ba ta mayar da martani ba kan wadannan zarge-zargen.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories