Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbubuwa 15 da Kwankwaso ya ce zai yi idan ya zama shugaban...

Abubuwa 15 da Kwankwaso ya ce zai yi idan ya zama shugaban kasa

Date:

 

By Mukhtar Yahya Usman

A ranar Talatar nan ne dan takar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da manufofin siyasarsa da kuma abinda zai yiwa al’umma idan ya zama shugaban kasa.

 

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ake ta sukar dan takarar da kin bayyana manufifinsa ga jama’a.

 

Sai dai an jiyo Kwankwaso na cewa ya boye manufofin nasa ne don gudun satar fasaha da ga wasu yan takara na daban, inda kuma ya yi alkawarin bayyana manufifin nasa ranar 1 ga Nuwambawar wannan shekara.

 

Haka kuma Kwankwaso ya bayyana manufofin nasa kamar yadda ya yi alkawari harma Premier Radio ta tsakuro muhimman abubuwa 20 daga cikinsu.

 

  1. Jagoranci da Adalci

 

Cikin takardar manufofin da kwankwason ya bayyana ya nuna cewa za a samar da Jagoranci na gari da Adalci yadda kowa zai ji ana damawa da shi.

 

  1. Zaman lafiya da Hadin-kai

 

Kwankwaso ya yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya da tsare rayuka da dukiyoyin jama’a inda ya ce zai magance matsalolin satar mutane, fasa bututun mai, rikicin manoma-makiyaya da dai sauransu.

  1. Farfado da tattalin arziki

 

Gwamnatin Kwankwaso za ta fito da tsare-tsaren gyara ta hanyar ceto tattalin arzikin kasa, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma kawo dabaru masu dorewa da za su kawowa kasa cigaba.

 

  1. Ilmi mai nagarta

 

Daga cikin alkawuran ‘dan takarar akwai farfado da ilmi, ya ce ba zai gina sababbin makarantu ba, amma za a maida hankali wajen inganta wadanda ake da su domin samun nagartaccen ilmi.

 

  1. Kiwon lafiya

 

Idan Kwankwaso ya kafa gwamnati, ya sha alwashin gyara bangaren kiwon lafiya a Najeriya. ‘Dan siyasar yace za a kara yawan malaman lafiya, kuma a cirewa mata kudin ganin likita.

 

  1. Lantarki

 

‘Dan siyasar ya fahimci sai da wannan ne za a habaka tattalin arziki, ya ce zai tabbatar an samu isasshen wutar lantarki mai arha da dorewa ta yadda za a kawowa Najeriya cigaba.

 

  1. Magance talauci

 

Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zai tabbata abinci, ilmi da tufafi da sauran abubuwan more rayuwa ba su fi karfin talaka a kasar nan ba.

 

  1. Abubuwan more rayuwa

 

Wani alkawari da Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka shi ne gwamnatinsa za ta kawowa kowanne yanki cigaba, ya ce za ayi wa dukkan wani bangare adalci wajen samar da abubuwan more rayuwa.

 

  1. Bin doka da Oda

 

Kwankwaso ya yi alkawari ba za a rika yi wa doka hawan kawara ba, ya ce dokar kasa za ta yi aiki a kan kowa, kuma kowa zai sha romon demukradiyya.

 

  1. Hulda da kasashen ketare

Daga cikin manufofin Rabiu Kwankwaso shi ne ya gyara kallon da ake yi wa Najeriya a Duniya, kuma ya inganta alakarmu da sauran kasashe, ya sa Najeriya jagoranci a fadin nahiyar Afrika.

 

  1. Aikin gwamnati ‘Yan fansho

 

‘Dan siyasar ya yi alkawarin ba zai yi watsi da hakkokin dattawan da suka yi wa kasa wahala da kuruciyarsu ba, sannan ya ce zai gyara aikin gwamnati, ya dawo masa da kimar da ya yi a baya.

 

  1. Harkar noma da abinci

 

Za a sa ran idan jam’iyyar NNPP ta karbi mulki a samu isasshen abinci ta hanyar zamanantar da aikin gona. ‘Dan takaran ya tabo harkar noma da kiwon dababbobi domin bunkasa sha’anin gona.

 

  1. Mallakar gida Baya ga hakkin tsofaffin ma’aikata.

 

Kwankwaso ya ce zai maida hankali wajen ganin mallakar gida ya yi sauki ta hanyar hada-kai da bankuna da kuma gina gidaje ga al’umma.

 

  1. Miyagun kwayoyi

 

Wani bangare da takardar manufofin ‘dan takaran ta duba shi ne ‘yan shaye-shaye. Gwamnatin NNPP za ta magance wannan matsala wanda tushe ce wajen kawo rashin tsaro da tattalin arziki.

 

  1. Muhalli

 

Manufofin ‘dan takaran sun duba matsalar sauyin yanayi da muhallin al’umma. Kwankwaso zai bada karfi domin takaita annoba irinsu ambaliya, kwararowar hamada da zaizayewar kasa.

 

Wannan wani bangare ne na wasu daga cikin manufofin da dantakarar ya bayyana zai mayar da hankali idan aka zaben shi shugaban kasa.

Latest stories

Related stories