Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano ta amince da rahoton wucin gadi kan gyaran kundin...

Majalisar dokokin Kano ta amince da rahoton wucin gadi kan gyaran kundin tsarin mulkin kasa

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da rahoton wucin gadi kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan ciki harda sauyawa karamar hukumar Kunci suna zuwa Tigari.

 

Gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan da ake son yin shine karo na biyar.

 

Majalisar ta amince da rahoton ne a zamanta na Talatar nan.

 

Da yake karin haske kan aikin, shugaban kwamitin gyaran kuma mataimakin shugaban majalisar Kabiru Hassan Dashi, ya ce, kwamitin ya shafe kimanin watanni shida wajen gudanar da aikin nasa.

 

Yace bangarori guda 44 za a gyara a kundin tsarin mulkin kasar nan wanda hakan yasa majalisar dokokin Kano ta bada shawarar amincewa da dokokin da za’a gyara.

 

Majalisar dokokin ta kuma amince da kafa shugabannin gudanarwar cibiyar koya wa matasa sana’o’i ta Aliko Dangote da ke nan Kano.

 

A ganawar sa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar shugaban masu rinjaye Labaran Abdul Madari, ya ce gwamnati bata da cikakken hannu wajen gudanar da makarantar.

 

Yace dokar ta bayyana cewa Mayan shekaru hudu za kuma a iya karawa shugabanin makarantar wasu shekaru hudun.

Latest stories

Related stories