Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwankwaso na iya bamu matsala - Alhassan Ado Doguwa

Kwankwaso na iya bamu matsala – Alhassan Ado Doguwa

Date:

Shugaban masu rinjaye na Majalisar wakilai, kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar kanan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado ya ce tasirin da Sanata Kwakwankwaso ke da shi a Kano ka iya basu matsala a zaben 2023.

 

Alhassan Ado ya bayyana haka ne a zantawarsa da BBC, kan batun rikicinsa da dan takarar mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo.

 

Ado Duguwa wanda aka rawaito sun samu sabani da Murtala Sule Garo a wani taron masu ruwa da tsaki na APC da ya gudana a gidan mataimakin gwamnan Kano Nasiru Gawuna a ranar Litinin.

 

Taron wanda aka shirya shi a gidan Gawuna domin duba nasarori da kuma matsalolin da APC ta samu a ziyarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu.

 

Da fari dai jaridar Daily Nigerian ta rawaito lamarin ya faru ne lokacin da Doguwa da ba a gayyace shi taron ba ya je ganin shugaban jam’iyyar APC na jiha, Abdullahi Abbas.

 

Inda Alhassan Doguwa yayi korafin cewa shugabannin APC sun mayar da shi saniyar-ware kan al’amuran da suka shafi jami’iyyar.

 

“Shakka babu muna fuskantar muguwar barazana yayin da ake tunkarar babban zaben Shekarar 2023”

 

“Ku sani kowa ya san tasirin da tsohon gwamnan Rabi’u Musa Kwankwaso yake dashi a Kano wanda hakan ka iya bamu matsala”, a cewar Alasan Ado Doguwa.

 

Tuni dai zaben Shekarar 2023 ke ci gaba da karatowa, wanda jami”iyyun siyasar kasar nan suke kokarin magance matsalolin da suke fuskanta.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories