Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMa’aikan Da Gwamnatin Kano Ta Dakatar Sun Fara Samun Albashi Bayan Mayar...

Ma’aikan Da Gwamnatin Kano Ta Dakatar Sun Fara Samun Albashi Bayan Mayar Da Su Bakin Aiki.

Date:

Wasu daga cikin ma’aikan da gwamnatin Kano ta dakatar sun fara samun albashi bayan mayar da su bakin aiki.

Gwamnatin Kanon dai ta dakatar da ma’aikatan su sama da dubu goma wadanda aka dauka aiki a karshen gwamnatin da ta gabata tare da dakatar da albashinsu.

Sai dai bayan tantancewa, gwamnatin Abba Kabir ta mayar da wasu daga cikin su, inda suka fara karbar albashin bayan korafe-korafen jan kafa da suka rika yi.

Kwamared Abdurrahman Yusuf Tarauni, shi ne shugaban kungiyar sabbin ma’aikatan da ke bibiyar hakkokin nasu, bayan kafe sunayensu sun fara samun albashi daga daren ranar Juma’ar da ta gabata.

Sai dai yace har yanzu akwai da yawa daga cikin ma’aikatan da kawo yanzu ba su samu albashin nasu ba.

Kawo yanzu dai gwamnatin Kano ba ta ce komai ba a kan lamarin.

Latest stories

Related stories