Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoFarashin Albasa Ba Zai Sauka Ba A Wannan Shekarar - Manoma

Farashin Albasa Ba Zai Sauka Ba A Wannan Shekarar – Manoma

Date:

Manoman albasa a jihar Kano sun ce farashin albasa ba zai yi saukar da ake tunani ba a bana duba da tsadar man fetur wanda da shi ne suke amfani domin injinan ban ruwa.

A zantawar sa da wakiliyarmu Hafsat Iliyasu Dambo, sakataren kungiyar manoman albasa na kasa reshen Kano, Mustafa Adamu, ya ce ko da farshin zai sauka to ba zai wuce da kashi 2 cikin 100 na farshinta na yanzu ba.

Yace suna hasahen albasar za ta kuma yi karanci sakamakon tsadar man fetur a kasar nan, domin da shi injinan ban ruwa ke amfani.

Mustafa Adamu, ya ce a tarihi ba a taba samun hauhawar farashin albasa kamar bana ba.

Al’umma musamman ma mata na ci gaba da kokawa sakamakon tashin farshin albasa wanda suke ganin kuma ita ce jigo wajen girki.

Latest stories

Related stories