Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Sauya Sunan Karamar Hukumar Kunci zuwa...

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Sauya Sunan Karamar Hukumar Kunci zuwa Ghari.

Date:

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da sauya sunan karamar hukumar Kunci zuwa Ghari.

Tabbacin hakan na kunshe ne cikin wata takarda da majalisar ta aikewa babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Kano mai kwanan watan 14 ga watan Disambar da muke ciki.

Da yake yiwa wakilinmu, Kamalu Umar karinbayani kan sauya sunan daga Kunci zuwa Ghari, shugaban karamar hukumar, Aminu Idi Shuwaki, ya ce tun bayan shigar sa Ofis, shi ne mutum na farko da ya fara yunkurin ganin an sauyawa karamar hukumar suna.

Ya ce kasancewar suna yana da muhimmanci a rayuwar kowane irin abin halitta, har ma da muhallan da dan adam yake rayuwa, kamar yadda addinin musulunci ya horar.

Shuwaki ya kara da cewa tun da farkon tarihi sunan garin nasu shi ne Kunci Gari, kafin daga bisani al’umma su mayar da sunan zuwa Kunci wanda a cewar sa hakan ka iya taba garin kai tsaye ta fannoni da dama.

Ya godewa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar sauyawa karamar hukumar suna, wanda ya ce abu ne da al’ummar garin suka dade suna jira tare da yin farin ciki da hakan.

Latest stories

Related stories