Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Sanar Da Daukar Matakin Hana Shoprite Ficewa...

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Sanar Da Daukar Matakin Hana Shoprite Ficewa Daga Kano

Date:

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sanar da fara daukar matakai domin dakatar da babban shagon sayar da kayayyaki na Shoprite daga rufe reshensa da ke nan Kano.

A makon da ya gabata ne Shoprite ya sanar da matakin ficewa daga Kano a watan Janairun sabuwar shekara, inda ya bayyana matsin tattalin arziki a matsayin dalilin hakan.

Wata sanarwa da mai bai wa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ismail Mudashir ya fitar, ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan shagon a makon nan a Abuja kan lamarin.

Sanata Barau, ya ce zai ga abin da zai iya yi domin karfafa musu gwiwa na ganin sun janye shawarar barin Kano, saboda akwai dumbin damammakin kasuwanci a jihar, da ya ce ta kasance cibiyar kasuwanci ta Arewa.

Ana dai ci gaba da samun ra’ayoyi dangane da hukuncin da shoprite din ya dauka na rufe shagon nasa dake Ado Bayero Mall a nan Kano, bayan ya fara gudanar da harkokin kasuwanci tun a watan Maris din 2014.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...