Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKwanaki hudu na mulkin gwamna Abba Kabir Yusuf yafi shekaru takwas na...

Kwanaki hudu na mulkin gwamna Abba Kabir Yusuf yafi shekaru takwas na mulkin Ganduje: Shugaban jam’iyar NNPP

Date:

Shugaban jam’iyar na NNPP ya ce kwanaki hudu na mulkin Abba Kabir Yusuf yafi shekaru takwas na mulkin Abdullahi Ganduje.

Shugaban jam’iyar NNPP na mazabar unguwar Nalado dake yankin Sharada Ibrahim Idris Muhd da ake kira Ibro Mai Rini, ne yayi wannan kira a ganawar sa da manema labarai.

Ganduje ya siyarwa da dansa kadarorin gwamnatin Kano sama da dari -NNPP|Premier Radio| 10.05.2023

Ibro Mai Rini, ya ce daga karbar mulkin Abba Kabir Yusuf abubuwa da yawa sun dawo hayyacin su a jihar Kano.

Ya ce yadda sabon gwamnan ke kai ziyara gurare da dama ya tabbatar da cewa zai kawo sauyi mai ma’ana a jihar Kano.

Karin ‘yan majalissar dokokin jihar Kano uku sun koma jam’iyar NNPP

Ibro Mai Rini, ya bukaci al’ummar jihar Kano dasu baiwa sabuwar gwamnati hadin kai don sauke nauyin dake kanta.

Shugaban jam’iyar NNPPn ya kuma bukaci gwamnatin Kano data tallafawa kananan ‘yan jam’iya da suka yi kokari wajen nasarar Kwankwasiyya.

InShot 20230602 100721706

Ibro Mai Rini, ya ce kananun ‘yan jam’iya sun sadaukar da lokutan su ba dare ba rana da kudin su wajen samun nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano.

Ya ce kananun ‘yan siyasa suna bukatar tallafi ta bangarori da dama kama daga jari domin cigaban kasuwancin su da kuma harkar ilimi a kan su da ‘ya’yan su.

Ibro Mai Rini ya ce da yawan su suna cikin mawuyacin hali kuma sun fuskanci gori da kyara saboda yadda suka sadaukar da kansu wajen tabbatar da cewa Kwankwasiya tayi nasara.

Ya ce hanyar da za a saka musu itace a tallafa musu da abin yi domin dogaro da kansu.

 

Latest stories

Related stories