Rahotanni sun bayyana cewa, Jam’iyyar NNPP a Kano, ta zargi gwamnatin APC karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da siyar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar.

Zargin wanda ake kallon gwamnatin jihar na siyar da kadarorin ga dan gwamna ba bisa ka’ida ba, abin da Jami’ar ta NNPP tace ba zata lamunta ba.

Har ma jami’iyyar ta ce za tayi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karbi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu.

Jawabin hakan na zuwa ne ta bakin shugaban kwamitin karbar mulkin jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata ziyara da yakai Hukumar Kano State Public Procurement Bureau a yammacin wannan Larabar.

Zargin da ke nuna cewa hukumar na cikin kadarorin gwamnati da aka siyarwa da dan gidan gwamna, akan kudi kimanin Miliyan 10, duk da cewa darajar hukumar ta kai Miliyan 50, a cewarsa.

Kawo yanzu dai bangaren gwamnatin Kano ba su magantu kan wannan Zargin da NNPP tayi ba.