Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKarin 'yan majalissar dokokin jihar Kano uku sun koma jam'iyar NNPP

Karin ‘yan majalissar dokokin jihar Kano uku sun koma jam’iyar NNPP

Date:

Wasu karin yan majalisar jiha Kano guda uku sun sauya sheka zuwa jamiyyar NNPP mai kayan marmari.

Sanarwar da daraktan yada labarai na Majalisar Uba Abdullahi, ya fitar a Larabar nan ta bayyana cewa shugaban majalisar injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karbi wasikar sauya shekar da ‘yan majalisun suka mika masa.

‘Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

‘Yan majalisun da sukai canjin shekar sun hada da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, day Muhammad Bello Butu-butu, mai wakiltar karamar hukumar Rimin Gado da Tofa, sai kuma Honorable Kabiru Yusuf Ismail mai wakiltar Karamar hukumar Madobi.

A yan kwanakin nan dai yan siyasar da aka batawa daga jam’iyyu daban-daban na komawa jamiyyar ta NNPP domin samun mafaka.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories