Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaAsibitin Aminu Kano ya kara kudin ganin likita da kudin wasu aikace...

Asibitin Aminu Kano ya kara kudin ganin likita da kudin wasu aikace aikace a asibitin.

Date:

Al’ummar jihar kano sun koka bisa ninka kudin ganin likita da sauran ayyukan da mahukuntan asibitin koyarwar na Malam Aminu Kano su kayi.

A ziyarar gani da ido da Premier Radio ta kai asibitin ta gano cewar marasa lafiya suna cikin mawuyacin hali la’ákari da matsin da ake ciki wanda hakan yasa suka ce ba zasu iya cigaba da biyan karin kudin ba.

An sace uwa da ‘yarta yayin rabon tallafi a Kaduna
Marassa lafiyar sun shaida cewar daga ranar juma’ar data gabata ne mahukuntan asibitin suka kara kudin.

Haka zalika mun tarar cewar kudin ganin likita ya ninka fiye da yadda yake a baya da kaso uku, inda a yanzu ake biyan naira 2100 kafin a duba marar lafiya.

Kudin gado da akan ajiye dubu ashirin mun gano cewar yanzu sai marar lafiya ya ajjiye dubu arba’in lakadan kafin a bash gadon.

Asibitin malam aminu kano ya kasance ja gaba a jerin asibitocin da ake alfahari dasu a arewacin kasar nan, biyo bayan taron kwararun likitoci dake lura da lafiyar al’umma.

Sai dai a wannan karon majinyata sun fara kauracewa asibitin, inda wasu ke neman sauya asibiti,wasu kuma suka hakura suka koma gida ba tare da an duba su ba.

Hajiya laraba da ta kawo danta asibitin domin ayi mishi aiki ta bayyanawa Premier Radio cewar an shaida mata kudin aikin naira dubu 150 da aka yanke da fari ya ninka zuwa naira dubu 300 a yanzun, wanda hakan yaje fata cikin tsananin tashin hankali yanda zata cika ragowar kudin.

Wani magidanci daya kawo matarshi awon ciki ma ya shaida cewar sun tarar awon cikin ya koma 28,000.

Sai dai mun tarar harta ma’ aikatan asibitin basu san daliliba kara kudin ba, abun da suke cewa kadai shine umarni ne daga sama kuma basu da katabus akai.

wani maáikaci a asibitin da yaki yarda mu nadi muryarshi ya kuma nemi a sakaya sunan shi yace an samu marassa lafiya da dama da suka fasa ganin likitan.

Kan hakan ne muka tuntubi mai magana da yawun asibitin Hajiya Hauwa Abdullahi domin muji dalilin yin karin kudin amma bamu samu jin ta bakinta ba har zuwa lokacin kammaluwar wannan rahoto sai dai tayi mana alkawarin zata bayyana matsayar asibitin a nan gaba kadan.

Latest stories

Related stories