Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Sunday, April 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDaliban makarantu gwamnati a jihar Zamfara ba zasu rubuta WAEC ba.

Daliban makarantu gwamnati a jihar Zamfara ba zasu rubuta WAEC ba.

Date:

Daliban makarantu gwamnati a jihar Zamfara ba zasu rubuta WAEC ba.

Yayin da ake shirin fara rubuta jarabawar kammala sakandire ta yammacin afurka (WAEC) a ranar 16 ga watan mayun da muke ciki zuwa 23 ga watan Yuni a kasar nan makarantun gwamnati a jihohin Sokoto da Zamfara basu mikawa hukumar dake shirya jarabawar sunan koda dalibi daya da zai rubuta jarabawar ba.

Kotu ta daure lauyan bogi wata 18 a Zamfara

Shugaban hukumar a kasar nan Patrick Areghan, ya bayyana haka a Litinin din nan a Lagos yayin da yake bayyana irin shirin da sukayi na rubuta jarabawar.

Ya ce makarantu masu zaman kansu ne kawai sukayiwa dalibai rijistar rubuta jarabawar inda yace basu da masaniya kan dalilin da yasa makarantun gwamnati basu bada sunayen daliban da zasu rubuta jarabawar ba.

Dalibai miliyan daya da dubu dari shida ne sukayi rijistar rubuta jarabawar ta WAEC daga makarantu dubu ashirin da dari biyu da ashirin da daya a kasar nan.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories