Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai2023: Akwai yiwuwar APC ta rasa damar shiga zabe mai zuwa- Masana

2023: Akwai yiwuwar APC ta rasa damar shiga zabe mai zuwa- Masana

Date:

Hafsat Bello Bahara
Wani masanin shari’a Barrister Ibrahim Kiyawa ya ce akwai yiwuwar Jam’iyyar APC ta yi asarar shiga babban zaben da ke tafe.

Masanin shari’ar ya ce matukar masu rike da mukamai a cikin gwamnati basu sauka daga mukamansu ba to ko shakka Jam’iyyar za ta samu matsala.

Sabuwar dokar zabe dai a sashe na 84 ta ce dole ne duk wanda ke rike da mukami a gwamanti kuma yake son tsayawa takara ya sauka kafin zaben fidda gwani na Jam’iyyarsa sannan ya tsaya takarar.

An jima dai ana kai ruwa rana akan sashen na sabuwar dokar da shugaban kasa ya rattabawa hannu a watan Fabrairu.

Wasu dai na ganin tabbatar da sashen zai taimaka wajen karfafar demokradiyar kasa, yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin dakile hakkin ‘yan kasa.

Wanan ce ma ta sanya wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa a kasar nan ciki har da shugaba Muhammadu Buhari suka soki wannan dokar, da har ta kai ga wasunsu sun shigar da kara kotu.

Cece-kuce bisa alfanun wannan dokar na cigaba da yin kamari biyo bayan ayyana neman takarar da wasu ministoci sukayi a kwanan baya alhalin basu ajiya mukaman nasu ba.

Barista Kiyawa ya ce shigar ministocin cikin zaben fidda gwanin APC tamkar cire jamiyar ne daga zabe mai zuwa matukar kotu ta yanke hukuncin halarta sashen na 84.

A cewarsa hukumar zabe ta kasa INEC ba za ta kara musu lokaci ko ta sake yi musu sabon zaben fidda gwani ba.

Gujewa faruwar hakan ne ma ya sanya jam’iyar ta APC ta hana su shiga cikin masu fitar da madafun iko ya yin babban taron da jamiyar ta gabatar.

A halin yanzu ana cigaba da dakon hukuncin kotu na karshe game da sashin dokar.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...