Saurari premier Radio
40.8 C
Kano
Monday, April 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKADUNA: Sanata Shehu Sani ya nemi a hadashi muhawara da dan takarar...

KADUNA: Sanata Shehu Sani ya nemi a hadashi muhawara da dan takarar gwamna a jam’iyar APC

Date:

Sanata Shehu Sani, ya nemi a hadashi muhawara da wanda jam’iyar APC zata tsayar amatsayin dan takarar gwamna a jihar Kaduna.

‘Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya kuma dan takarar gwamna a jam’iyar PDP Sanata Shehu Sani, ya ce ya kosa a hadashi yin muhawara a bainar al’umma tare da duk wani dan jam’iyar APC da za a baiwa tikitin tsayawa takarar gwamna a jihar.

Sanata shehu sani ya bayyana hakane a shafin san a Facebook a Litinin din nan.

Ya ce akwai maganganu a bakin sa masu zafi da daci kuma jama’a zasu so suji su.

“Wallahi na kosa muyi muqabala a bainan jama’a da Duk dan APC da za’a baiwa ticket na Kaduna;Akwai maganganu masu zafi da dachi daki daki da make jiransu dashi. Jama’a zasu ji abun da basu taba ji ba. Babban rufin asirin su,Idan bani Allah ya baiwa ba,” a cewar Sanata Shehu Sani.


Sanata Shehu Sani, dai ya sayi fom na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar adawa ta PDP a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

 

A kwanakin bayane dai gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’I ya bayyana Sanata Uba Sani a matsayin wanda zayyi takarar gwamna a jam’iyar APC a jihar Kaduna.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories