Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBarau ya fasa takarar gwamna, ya sayi fom din sanata

Barau ya fasa takarar gwamna, ya sayi fom din sanata

Date:

Mukhtar Yahya Usman

SanataBarau Jibril ya sayi fom din takarar Sanatan Kano ta Arewa a jam’iyyar APC a kokarinsa na sake komawa kam kujerarsa.

Sanata Barau ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
Wanann dai na zuwa ne kasa da awannin 24 bayan da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zabi mataimakinsa a matsayin mai gadonsa.

Wannan dai na zuwa ne gabannin rade radin da akeyi na sayen fom din senatan da Ganduje akace zai yi ayau na kakarar kujerar da Barau yake nema a yanzu.

Idan za a iya tunawa a baya sanata Barau ya nuna sha’awar sa ta tsayawa gwamnan Kano, sai dai gwamnan Kano bai mara masa baya ba.

Haka kuma yana daya daga ciki na gaba gaba da suka kafa kungiyar G7 a jam’iyyar APCn Kano karkashin Ibrahim Shekaru

Latest stories

Related stories