Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje zai sayi fom din takarar Sanata

Ganduje zai sayi fom din takarar Sanata

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Anasa ran magoya bayan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje za su saya masa fom din tsayawa takarar sanatan Kano ta Arewa.

Wannan dai na nuna gwamnan zai nemi kujerar sanatan Barau Jibril ke nan.

Ana ta rade radin cewa magoya bayan gwamnan ne ake sa ran za su saya masa fom din ranar Litinin.

Hakan dai, ya biyo bayan taron da aka yi tare da masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a fadar Gwamnatin Kano ranar Lahadi.

Kazalika, yayin taron kuma, an cim ma matsayar amincewa da Mataimakin Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaji Gwamnan.

Haka kuma tsohon kwamishinan Kananan hukumomi Murtala Sule Garo zai kasance mataimakin gwamnan.

Yanzu haka dai Sanata Barau Jibrin ne ke wakiltar mazabar a Majalisar Dattijai.

Sai dai tun bara yake takun-saka da Gandujen shi da wasu ’yan majalisa da ke wa kansu lakabi da G-7.

Dukkan su na aiki ne karkashin Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau.

Sai dai a ranar Juma’a Kotun Koli ta kawo karshen takaddamar, inda ta tabbatar da shugabancin tsagin Gwamna Ganduje, karkashin Abdullahi Abbas.

Sanata Barau dai wanda tuni ya bayyana aniyar shi ta neman takarar Gwamnan Kano ya ce zai ci gaba da zama a jam’iyyar ta APC

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...