Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

‘Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Date:

Aƙalla mutum 10 ne daga cikin mambobin majalisar dokokin jihar Kano suka sauya sheka daga Jam’iyyar PRP zuwa Jam’iyyar NNPP.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran majalisar Uba Abdullahi ya fitar ranar Juma’a.

Uba Abdullahi dukkanin mambobin sun aike da rubutacciyar wasika ne zuwa ga kakakin majalisar da ke bayyana sauya Shekar tasu.

A cewarsa wa su daga cikin dalilan da suka bayar sun hada da rikicin da ake fama da shi a cikin jam’iyyar tasu a matakan jiha da ma tarayya.

’Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Isyaku Ali Danja (Gezawa), Umar Musa Gama (Nassarawa), Aminu Sa’adu Ungogo (Ungogo), Lawan Hussain Chediyar ’Yan Gurasa (Dala) da kuma Tukur Muhammad (Fagge).

Sauran sun hada da Mu’azzam El-Yakub (Dawakin Kudu), Garba Shehu Fammar (Kibiya), Abubakar Uba Galadima (Bebeji) da kuma Mudassir Ibrahim Zawaciki (Kumbotso) sai kuma Yusuf Babangida(Gwale)

Idan za a iya tunawa, a ranar 29 ga watan Afrilu ne Majalisar ta sanar da sauya shekar mamba mai wakiltar mazabar Birni da Kewaye, Salisu Gwangwazo daga PDP zuwa APC, shi ma saboda rikicin cikin gida a PDP

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...