Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSalihu Tanko Yakasai ya kaddamar da takarar gwamnan Kano

Salihu Tanko Yakasai ya kaddamar da takarar gwamnan Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman
AlhajiSalihu Tanko Yakasai, tsohon mashawarcin gwamnan Kano ya Kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kano.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana aniyar tasa ne ranar Juma’a a nan Kano.

Ya Kaddamar da takarar ta sa ne karkashin Jam’iyyar PRP mai alamar Dan mukulli.

A jawabinsa Yakasai ya ce ya fito takarar gwamnan ne domin fitar da al’ummar awwKano daga cikin muwuyacin halin da suke ciki.

Ya ce akwai tsare-tsare da ya tanada Waɗanda zai gabatar Idan ya zama gwamnan Kano.

” Idan Allah ya bamu damar zama gwamnan kano zan tabbatar na yi Amfani da manufofin jam’iyyar P R P
“Mafi yawa daga cikin shugabanni a kasar nan sun sauka daga manufofin jam’iyyar su da aka zabe su a cikinta”.

Yace Kowa ya shaida irin aiyukan da gwamnonin jam’iyyar P R P na baya suka gudanar a jihohin Kano da Kaduna.

A cewarsa Abubakar Rimi ya yi aikin da har yanzu ba a samu gwamnan da ya yi aiki kamar sa a Kano ba.

” Bayan na fice daga jam’iyyar APC, masoya da magoya bayana sun yi ta kawo shawarar mu Koma PDP da sauran jam’iyyu har ma da jam’iyyun yarabawa, Amma bayan na yi addu’a na sami nutsuwar mu Koma jam’iyyar P R P.”

Ya Kuma bada tabbacin zai bijiro da aiyukan da za su inganta rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...