Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta daure lauyan bogi wata 18 a Zamfara

Kotu ta daure lauyan bogi wata 18 a Zamfara

Date:

Wata kotun majistare da ke zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ta tisa keyar wani lauyan bogi, Mista Chukwuka Jude, zuwa gidan gyaran hali na tsawon shekara daya da rabi.

PREMIER RADIO ta ruwaito Alkalin kotun, Sa’ad Garba, ya yanke wa lauyan bogin hukuncin dauri ne tare da cin sa tarar kudi N50,000.

Mista Chukwuka Jude dai bai bata lokaci ba wajen amsa tuhume-tuhumen da ake masa a gaban kotun.

An cafke Jude ne kan zargin aikata laifin yin sojan gona a matsayin lauya, yana zambatar mutane.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta kama shi ne bayan samun bayanan sirri kan yadda Jude yake damfarar mutane.

Lauyan bogi ya kirkiri katin shaidar bogi na lauya, ya bude ofis da kuma hada-hadar harkar shari’a na bogi wanda hakan ya ba shi damar damfarar mutane.

Bayan shigarsa hannun ’yan sanda, lauyan bogin ya yi yunkurin ba su cin hancin N300,000 don su sake shi amma suka ki, suka mika shi kotu.

Sai dai lauyansa ya bukaci kotun ta yi wa wanda ake kara sassauci, saboda tarihi ya nuna bai taba aikata wani laifi ba.

Lauyan nasa ya bukaci kotun ta duba hukuncin da ta yanke masa, tare da sauya shi da tara.

Sai dai alkalin kotun ya ki aminta, inda ya bayar da umarnin tisa keyarsa zuwa gidan gyaran hali.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories