Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotun daukaka kara ta sanya ranar fara shari’ar Yunusa Yellow

Kotun daukaka kara ta sanya ranar fara shari’ar Yunusa Yellow

Date:

Kotun daukaka kara da ke garin Fatakwal ta sanya ranar 17 ga Maris domin fara sauraron karar da Yunusa Yello ya daukaka a gabanta na kalubalantar hukuncin babbar kotun jihar Bayelsa.

PREMIER RADIO ta ruwito guda  daga cikin lauyoyin Yunusa Yellow Sunusi Musa ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Sauran lauyiyon da za su tsayawa Yunusa Yellow sun hadar da Huwaila Muhammad, Abdul Muhammad Rafindadi, da kuma Kayode Olasebikan.

Yadda shari’ar ta ke

Idan za a iya tunawa tun a shekarar 2015 ne aka kama Yunusa Yellow bisa zargin sato wata yarinya Ese Oruru da ga jihar Bayelsa zuwa Kano.

Yunusa Yellow dai ya taho da yarinyar Ese ne zuwa Kano suka kuma yi aure, sai dai an kama shi da laifin satar mutane, da kuma safarar kananan yara.

Bayan kama shi ne a nan Kano aka kuma aike da shi can jihar Bayelsa garin da yarinyar ta ke don a yanke masa hukunci.

Babbar kotun jihar dai ta zargeshi da laifuka har guda biyar da suka hadar da garkuwa da mutane, hakkewa karamar yarinya, da kuma yin amfani da dama kan karamar yariwa, sai kuma laifin yin amafani da karancin shekarunta wajen yi mata wayo.

A don hakan ne kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 26 a gidan yari a can Bayelsa.

Sai dai da yake yanke hukunci alkalin kotun  Jane Inyanga ta ce Yunsa bai aikata laifi na farko ba wato garkuwa da mutane.

Har ila yau mai shari’ar ta kama shi da laifin safarar mutane, da hakkewa karamar yarinya, da kuma yin amfani da girmansa wajen yiwa karamar yarinya wayo.

Bayan yanke hukunci ne kuma, Yunusa Yellow ya dauka kara domin neman hakkinsa.

Haka kuma kotun daukaka karar ta sanya ranar 17 ga Maris domin fara suararon karar da ya shigar.

Latest stories

Related stories