Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn sace uwa da 'yarta yayin rabon tallafi a Kaduna

An sace uwa da ‘yarta yayin rabon tallafi a Kaduna

Date:

‘Yan bindiga sun sace wata mata da ‘yarta yayin da suke rabon kayan tallafin azumin Ramadan ga mutanen kauye.

‘Yan bindigar sun sace Ramatu Abarshi, da ‘yarta Amira ne yayin da suke tsaka da rabon kayan tallafi ga mutanen garin Mariri dake karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.

2023: Kwankwaso zai yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP
Wani makusancin ta da ya nemi a sakaye sunan ta ya ce ‘yan bindigar sun bibiye su a jiya Asabar a kusa da kasuwar Magani a karamar hukumar Kachia dake kudancin Kaduna.

Ramatu Abarshi, dai tsohuwar shugabar sashen ilimin harkokin lantarki ce ta kwalejin kimiya da fasaha dake Kaduna.

Sai dai bayan da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Kaduna Muhammad Jalige, yace bashi da masaniya kan lamarin.

“Kasan mutane basa sanar da irin wadannan abubuwa ga ‘yan sanda da zarar sun faru,” a cewar sa.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories