Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai2023: Kwankwaso zai yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP

2023: Kwankwaso zai yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP

Date:

Jam’iyyar NNPP ta ce saura kiris tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa cikinta gabanin zaben 2023.

Sakataren NNPP na kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major, ya bayyana wa taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar a ranar Talata cewa Kwankwaso zai dawo jam’iyyar ce tare da tafiyar siyasara ta TNM da kuma magoya bayansa.

“Na san ’yan Najeriya na ta hasashe, to ina tabbatar muku cewa mun yi nisa da tattaunawa da Kwankwaso, har mun kusa kammalawa; Nan da ’yan kwanaki za mu sanar da su inda aka kwana; Amma tabbas saura kiris Kwankwaso ya sauya sheka zuwa NNPP,” a cewarsa.

Major, ya shaida wa taron da jam’iyyar ta shirya domin tunkarar zaben 2023 cewa Kwankwaso ya ba da tabbacin cewa zai kasance dan jam’iyya mai biyayya tare da bin dokokinta kamar kowane dan jam’iyya.

Kasa da mako biyu ke nan da tsohon gwamman Kanon ya assasa tafiyar siyasa ta TNM wadda ya jagoranci taron kaddamar da ita a Abuja.

Kawo yanzu dai babu wani martani da daga bangaren TNM ko Kwankwaso game da sauya shekar zuwa NNPP.

A kwanakin baya Aminiya ta kawo rahoton cewa jam’iyyar APC mai mulki na zawarcin Kwankwao ya sake dawo cikinta gabanin zaben 2023.

Wasu makusantan Kwankwaso sun bayyana cewa tattaunawa tsakanin bangarorin ta yi nisa, amma ba a cimma matsaya a kan batun ba, wanda ake zaton a karkashinsa, Kwankwaso zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Mataimakin Shugaban Kasa mai ci, Yemi Osinbajo.

Kwanaki kadan bayan hakan ne tsohon Ministan Tsaron da abokan siyasarsa suka kaddamar da tafiyar siyasa ta TNM, wadda ake sa ran za su yi amfani da ita domin yin hadin gwiwa da wata jam’iyya domin kaiwa ga manufarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Sai dai a yayin kaddamar da TNM, Kwankwaso ya bayyana cewa APC da jam’iyyarsa ta PDP ba su ne famita ga al’ummar Najeriya ba.

Babu takarar kai-tsaye

Agbo ya ce NNPP ba za ta ba wa tsohon ministan tsaron tikitin tsayawa takarar shugaban kasa kai-tsaye ba, za ta ba wa sauran masu sha’awa damar gwada farin jininsu.

“Babu batun ba wa Kwankwaso tikitin takarar shugaban kasa kai-tsaye, kuma ya shaida mana cewa ba ya kaunar a dauka cewa ya shigo NNPP ne domin kawai ya samu tikitin takarar shguaban kasa.

“Mun ba wa sauran masu neman takara kwarin gwiwa su fito su gwada irin farin jininsu da kuma yin amfani da ’yancinsu na tsayawa takara da na jama’a na zaben wanda suke so,” inji Agbo Major.

NNPP ba ta yi hadin gwiwa ba

Ya kuma yi watsi da batun yiwuwar jam’iyyar za ta yi hadin gwiwa ko kuma ta hade da wata jam’iyya ko kungiya, saboda a baya ta yi hakan, amma bai tsinana mata komai ba.

“Mun sha ganin abubuwa, kuma ba mu yarda da hadin gwiwa ba, domin mun jaraba a 2007 inda muka kulla kawance a lokacin zaba, amma hakarmu ba ta cim-ma ruwa ba.

“Hadin kai ya kunshi dunkulewa a kafa sabuwar jam’iyya ko kuma kulla kawance. Mun jaraba kawance amma ba su samu wani sakamakon da za a yaba ba, abin da ya rage yanzu kawai shi ne hadewa,” a cewarsa.

Game da taron kuma, Agbo Gilbert Major ya ce, “’Yan Najeriya na ta shirya wa zaben 2023, shi ya sa muka kira wannan taro domin sauya wa jam’iyyar fasali da samun karin damammaki.

“Karin ’yan Najeriya na ta shigowa, wanda hakan ke bukatar a yi maraba tare da yin la’akari da irin bukatun masu shigowar.

“Wadannan su ne muhimman shawarwarin da za mu dauka domin tsara babban tsaron jam’iyyarmu da za a cikin kwana 30 masu zuwa.”

A lokacin taron, shugaban jam’iyyar na farko, Dokta Boniface Okechukwu Aniebonam, ya sanar da cewa zai sauka daga mukaminsa a matsayin wani bangare na kawo sauye-sauye a jam’iyyar domin ta cim-ma abin da ta sa a gaba.

A cewarsa, yawan shekarunsa da yanayin lafiyarsa ba za su bari ya yi aiki  yadda ya kamata ba a matsyin Shugaban jam’iyyya

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories