Mata da dama ne suka mamayen Kofar majalisar kasar nan biyo bayan watsi da aka yi da bukatunsu jiya Talata a zauren Majalisar.
A jiya ne ‘yan majalisar suka fara kaɗa ƙuri’a kan wasu ƙudirori da aka gabatar na gyaran kundin tsarin mulki, ciki har da wanda ya nemi a bai wa matan kashi 35 cikin 100 na muƙaman siyasa.
Sai dai amma ‘yan majalisar sun yi watsi da kudirin.

Matan da suka taru ƙarƙashin ƙungiyoyi daban-daban, sun ce zaman dirshan za su yi a bakin ƙofar.
“Ba za mu bar wajen nan ba har sai mun ga shugaban majalisa, sai majalisa ta bai wa mata ‘yancinsu,” a cewar Niri Goyit daga ƙungiyar Action Aid.
Lamarin ya faru duk da cewa Matar Shugaban Ƙasa Aisha Buhari ta je majalisar da kanta a makon da ya gabata don ganewa idonta da kuma tabbatar da cewa ƙudirorin mata sun samu karɓuwa a gyaran kundin tsarin mulkin.
A yau Laraba ne ‘yan majalisar za su kammala kaɗa ƙuri’a kan batutuwa kusan 60 da suka shafi gyaran ɓangarori daban-daban na kundin mulkin.