Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciJirgin Qatar ya fara suka a Kano

Jirgin Qatar ya fara suka a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Qatar Airways ya fara sauka a birnin Kano  a yau Laraba.

 Jirgin ya sauka cikin murna da annashuwa daga hukumomin ƙasar  nan da kuma kamfanin.

Jirgin Boeing 787 ya sauka a babban filin jirgi na Mallam Aminu Kano (MAKIA) da misalin ƙarfe 11:00 da ɗoriya.

Jekadan Najeriya a ƙasar Qatar, wadda ta mallaki kamfanin, Ahmadu Yakubu Abdullahi na cikin waɗanda suka halarci bikin saukar jirgin karon farko a tarihi.

Kano ce wuri na uku a kasar nan da kamfanin zai dinga sauka bayan Abuja da Legas.

A gobe Alhamis kuma zai ƙarasa birnin Fatakwal na Jihar Rivers.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...