Hukumar Karota tayi afuwa ga wadanda aka kama da laifin keta dokar hukumar a kan tituna a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Mai magana da yawun hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa, ne ya bayyana haka a wata tattaunawar sa da Premier Radio da a yammacin ranar Lahadi.
Ya ce shugaban hukumar Baffa Babba Dan’agundi ne ya bada umarnin domin kyautatawa al’umma alfarmar wannan wata.
Yace amma hakan ba yana nufin ba za a kama mai laifi ba ne, sai dai hukunci ne aka dakatar, amma ana nasiha tare da bada shawara domin a kiyaye a gaba.
KAROTA za ta fara kama ‘yan sahun da basu da koriyar lamba a tantinsu
Kofar Na’isa, ya kuma ce sassaucin dokar bai shafi masu kasa kayan siyarwa a bakin titi da kuma wadanda ke tsayawa a guraren da aka hana tsayawa ba.
Sai dai Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, ya ce hukumar zata cigaba da hukunta masu ababen hawan dake karya doka da zarar watan azumin Ramadan ya wuce.