Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKAROTA za ta fara kama 'yan sahun da basu da koriyar lamba...

KAROTA za ta fara kama ‘yan sahun da basu da koriyar lamba a tantinsu

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar KAROTA ta ce, za ta ci gaba da kama duk Adaidaita sahun da ba a rubuta Koriyar Lamba ɓaro-ɓaro a saman Tantinsa ba.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Naisa ya fitar yau Litinin.

Sanarwar ta ce Hukumar ta lura da galibin baburan Adaidaita Sahun da aka kama da aikata manyan laifuka ba sa rubutu Lambarsu ɓaro-ɓaro a jikin tantin ba.

Ta ce hakan ya zama wajibi ta ɗauki matakin tilastawa direbobin rubuta lambar don sauƙaƙawa al’umma masu hawa Ɗan Sahu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin al’umma masu kishin jihar nan ne suka an-karar da Hukumar da nufin ɗaukar matakin da ya kamata domin a shawo kan matsalar.

Nabilisi ya kuma shaida cewa ƙofar Hukumar a ɓude take ga duk waɗanda suke da wani ƙorafi ga matuƙa Baburan adaidaita sahun, da su gabatar da shi ga Hukumar domin ɗaukar matakin daya dace.

Ya kuma yi kira ga ɗaukacin al’umma masu hawa baburan Adaidaita Sahun da su tabbatar sun kwafi ko hadda ce Koriyar Lambar da ke jiki baburan domin sauƙaƙewa Hukumar yin bincike idan buƙatar hakan ta
taso.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...