Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoHukumar kula da asibitoci ta Kano ta musanta kai hari asibitin Murtala

Hukumar kula da asibitoci ta Kano ta musanta kai hari asibitin Murtala

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta musanta cewa wasu yan daba sun kai hari asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke nan Kano.

Shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar Ibrahim Abdullahi ne ya musanta hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce babu wata hujja mai karfi har yanzu da ta tabbatar da cewa an Kai hari Asibitin na Murtala.

Ya ce a bayanin da suka samu daga asibitin, wasu batagari ne suka ratsa ta cikin asibiti lokacin da jami’an Vigilante suka biyosu.

Sun kuma ratsa ta sashin bada agajin gaggawa na Asibitin domin gujewa kamun yan vigilante din.

A cewarsa ganin hakan ce ta sanya jama’a suka fara gudu saboda firgita, kuma babu wani dan daba da ya shiga Asibitin.

Idan za a iya tunawa dai a daren ranar Alhamis ne aka samu Rahoto yan daba sun shiga Asibitin na Murtala Inda suka dinga kwacewa jama’a kudi da wayoyi.

Latest stories

Related stories