Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAnji harbe-harbe a kusa da gidan Muhuyi Magaji

Anji harbe-harbe a kusa da gidan Muhuyi Magaji

Date:

A jiya Lahadi ne aka yi wata ba-ta-kashi tsakanin jami’an ‘yan sanda a jihar Kano da Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Rimingado.

Idan dai ba a manta ba, a watan Yulin bara ne aka dakatar da Muhuyi sakamakon zargin sa da wata badaƙalar kuɗi.

‘Yan sanda sun yi tsinke a gidan Muhuyi Magaji ne dake Yahya Gusau Road da misalin ƙarfe 7:00 na dare.

Mazauna yankin sun tabbatar da mamaye gidan da ‘yan sanda suka yi, suna masu cewa sun ji ƙarar bindiga a lokacin da ‘yan sandan suke ƙoƙarin kama Muhuyi.

“Mun ji ƙarar bindigogi, muka hango jami’an tsaro a kusa da gidan. Da misalin ƙarfe 9:30, muka ji ƙarar tayoyi a lokacin da suke ƙoƙarin su kori wata mota da take fitowa daga gidan”, in ji wani maƙobcin Muhuyi da ya buƙaci a sakaye sunansa.

Sai dai ba a sani ba ko ‘yan sandan sun kama Muhuyi ko kuma a’a.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories