33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiMasarautar Kano ta umarci hakimai su fara shirin bikin karamar Sallah

Masarautar Kano ta umarci hakimai su fara shirin bikin karamar Sallah

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Ibrahim Hassan Hausawa

Masarautar Kano ta bayar da umarni ga daukacin hakimanta da su kasance a cikin kwaryar birnin Kano domin gudanar da bikin hawa sallah Ƙarama na bana.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Awaisu Abbas Sanusi a madadin sakataren Masarautar.

Sanarwar ta kuma bukaci daukacin Hakiman da su taho cikin birni tare da Dagatansu, da dawakansu, da sauran mahayansu, a ranar Juma’a  28 ga Ramadan, dai dai da 29 ga watan Afrilu, 2022.

Kazalika sanarwar ta kuma umarci hakiman da suje Fadar Sarkin Kano a ranar Asabar 29 ga watan Ramadan, da karfe 11 na safe, domin karbar Umarni daga mai martaba.

Bayan wannan taro Hakiman za kuma su kara haduwa domin wani taro na musamman a dakin taro na musamman na Masarautar Kano, dake kofar Kudu domin yi musu bayani kan yadda Hawan zai kasance.

Tuni dai Masarautar Kano ta sanar da shugabannin ƙananan hukumomin Hakiman domin samun sauƙin gudanar da al’amuran da suka sanya gaba.

Latest stories