Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasiyar Tahir Fadlallah: "duk inda na rasu a dawo dani Kano a...

Wasiyar Tahir Fadlallah: “duk inda na rasu a dawo dani Kano a binne ni”

Date:

Qaribullah Abdulhad Namadobi

Tahir Fadlallah na cikin manyan yan kasuwa yan kasashen ketare da suka tallafawa tattalin arzikin jihar Kano, ya rasu yanada shekaru 78 a Beirut babban birnin kasar Labanan a safiyar yau juma’a.

Shine dai ya mallaki katafaran Otal din nan mai suna Tahir Guest Palace dake birnn Kano.

An kwantar dashi a wata cibiyar kula da lafiya a Beirut a sashin nan na gobe da nisa wato ICU tun a ranar 15 ga watan Afirilu da muke ciki.

An haifi Tahir Fadlallah a ranar 5 ga watan Fabarairu na shekarar 1948 a Beirut, ya kuma dawo jihar Kano tare da iyayensa tun yana dan shekaru 2 a duniya, inda yayi harkokinsa na kasuwanci a cibiyar Kasuwancin Najeriya Kano.

Jihar Kano dai nada tarihin karbar baki da kuma basu cikakkiyar dama domin gudanar da kasuwanci da sauran al’amurran rayuwa, hakan ne ya bawa mutane irinsu marigayi Tahir Fadlallah damar zama hamshakin dan kasuwa a jihar dukda kasancewarsa dan asalin kasar waje.

Mutanen da sukayi alaka da marigayi Tahir sun basa sheda da kasancewa mai son jihar Kano da kuma son cigabanta.

Ana kuma yaba masa matuka kan irin gwagwarmayar da yayi wurin kawowa jihar cigaba, hakan kuma yasa gwamnatin jihar ta taba karramasa.

Ya rasu ya bar matarsa da ƴaƴa 5, ya kuma bar wasiyyar cewa duk inda ya rasu, to a dawo dashi jihar Kano domin a binneshi.

Latest stories

Related stories