Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMun karbi korafin cin hanci da dama akan Muhyi-Kano Anti- curruption

Mun karbi korafin cin hanci da dama akan Muhyi-Kano Anti- curruption

Date:

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta karbi korafe-korafen cin hanci da rashawa a kan dakataccen shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado.

Mukaddashin shugaban hukumar Barr. Mahmoud Balarabe, ne ya bayyana hakan yayi da yake zantawa da manema labarai kan kamun da aka yiwa Muhyin.

Ya ce bayan dakatar da shi jama’a da dama sun kaiwa hukumar korafinsa, da suke da alaka da cin hanci da rashawa.

Yace sun tura masu korafin ga yan Sanda domin ayi binciken achan, Saboda gudun kada al’umma da shi wanda ake zargi su yi zaton hukumar ba za ta yi musu adalci ba.

Mahmoud Balarabe ya ce daga cikin korafin da aka gabatarwa Hukumar, akwai yadda Muhuyin ya yanka Wani fili a titin Yahya Gusau da Kuma na gonar wasu magada a unguwar farawa.

A cewarsa an kwace musu gonar, ita kuma hukumar ta kwato kudin ganar har Naira Miliyan 8, amma aka baiwa magadan Naira Miliyan 3 kachal.

Ya Kuma Kara da cewa akwai zargin karkatar da kudaden al’umma da ake tarawa a asusun Hukumar da aka gano bayan ya bar ofis.

Barr. Muhd Balarabe ya Kuma ba da tabbacin za su bi dukkanin Waɗannan korafe-korafe har zuwa Kotu domin tabbatar da Kotu ta yi hukunci akai.

Ya ce tun lokacin da ya karɓi ragamar Hukumar ake samun cigaba sosai ta fuskar karbar korafe-korafe aƙalla Guda 60 a kowacce rana.

Latest stories

Related stories