Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiA shirye nake a yi min gwajin miyagun kwayoyi -Dan Sarauniya

A shirye nake a yi min gwajin miyagun kwayoyi -Dan Sarauniya

Date:

Hafsat Bello Bahara

Daya daga cikin yan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP a nan Kano Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya yace a shirye yake a yi masa gwajin shan miyagun kwayoyi.
Ya ce hakan cigaba ne wajen tabbatar da an samar da yan takarar da suka chanchanci su jagoranci alumma.

Dansarauniya ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan dokar da hukumar  NDLEA, ta yi na yiwa dukkan masu neman takara gwajin shaye-shayen miyagun kwayoyi don tabbatar da nagartar shugabannin da za a zaba.

Tuni a’lumma suka shiga bayyana ra’ayiyon su game da kudurin da hukumar NDLEA ta fitar a tun a ranar Larabar da ta gabata na tantance dukkan wani mai son yin takarar a babban zabe mai zuwa na 2023.

Da yake bayyanawa Premier Radio ra’ayinsa kan batun Mu’azu Magaji ya ce dukkan wanda ya tabbatar baya ta’amali da kwaya ba zai yi fargabar zuwa a tantance shin ba.

Ya ce akwai bukatar a inganta tsarin gwajin domin tabbtar da wasu basu bi ta bayan gida su tsallake ba tare da anyi musu sahihin gwaji ba.

Shima shugaban hukumar ta NDLEA reshan jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya shaidawa Premier Radio cewa ba a dauki wannan matakin da zummar muzgunawa ko cin fuskar wani dan siyasa ba.

A cewarsa shugaba kamar madubi yake a wajen al’ummarsa, saboda haka akwai bukatar samar da shugabanni na gari domin al’umma suyi koyi dasu.

Alumar jihar Kano da dama sun nuna jin daɗinsu da wannan kudirin, wanda suke ganin shi ne haya daya tilo da za a tace bara gurbi tsakanin yan takara a zaben dake tafe na 2023.

Latest stories

Related stories