Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta bada umarnin a binciki Abdullahi Abbas

Kotu ta bada umarnin a binciki Abdullahi Abbas

Date:

Babbar kotun tarayya dake nan Kano ta bada umarnin a kamo shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas bisa zargin kalaman tunzuri da cin mutunci.

 

Alkalin kotun, mai sharia’a Abdullahi Muhammad Liman ne ya bada wannan umarni a jiya Juma’a bayan korafin da jam’iyyar NNPP tayi ta bakin dan takarar gwamnan ta Abba Kabir Yusuf.

 

Abba Kabir Yusuf tun da fari ya bukaci kwamishinan ‘yan sandan Kano ya bunciki shugaban jam’iyyar APC bayan kalaman tada zaune tsayen sai dai, kwamishinan yayi burus da bukatar ta su,hakan yasa suka shigar da kara gaban kotu.

 

Lauyan NNPP Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci ya bayyanawa Premier Radio cewa kotun ta bada umarnin ‘yan sanda su binciki Abdullahi Abbas su kuma gabatar dashi a gaban ta.

 

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 30 ga watan Janairun da muke ciki domin cigaba da sauraran shari’ar.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...