Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWike yayi barazanar hana Atiku yakin neman zabe a filin wasa na...

Wike yayi barazanar hana Atiku yakin neman zabe a filin wasa na jihar Rivers

Date:

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya yi barazanar soke izinin yin amfani da filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, babban birnin jihar, wanda ya ba dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar domin yakin neman zabe.

 

Gwamna Wike ya ce sama da wata daya kenan darakta-Janar na yakin neman zaben Atiku a jihar Rivers, Dokta Abiye Sekibo, na sintiri a filin gabanin taron da za su gudanar ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa.

 

Wike ya ce sun ba da filin domin gudanar da taron ba tare da an biya su ko sisi ba, inda ya ce za a damka musu shi ana saura kwana biyu kafin ranar taron.

 

Sai dai yayin gangamin yakin neman zaben PDP a Karamar Hukumar Oyigbo da ke Jihar ranar Juma’a, Gwamnan ya ce Abiye ba shi da hurumin da zai karbe wajen tun ana saura wata daya kafin ranar taron nasu.

 

Ya ja kunnen dan siyasar da kada ya fusata su ta hanyar yunkurin karbe filin, wanda mallakin Gwamnatin Jihar ne tun ana makonni kafin ranar, in ba haka ba kuma su soke izinin.

Latest stories

Related stories