Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar gwamnoni sun gana da Gwamnan CBN kan sauya tsarin kudi a...

Kungiyar gwamnoni sun gana da Gwamnan CBN kan sauya tsarin kudi a kasar nan

Date:

Yayin da batun sauyin fasali kudin ke kara zama da babban abin Tattaunawa a kasar nan Kungiyar gwamnonin kasar nan ta kafa wani kwamiti mai mambobi shida da zai yi aiki da babban bankin kasa CBN don magance matsalolin da ke faruwa a tsarin tafiyar da hada-hadar kudi.

 

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin jawabin bayan taro da ta fitar a yau Asabar bayan wata ganawa da ta yi da Gwamnan Babban Bankin CBN, Mista Godwin Emefiele, ta kafar internet.

 

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnoni ta kasa kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya kunshi gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, a matsayin shugaba.

 

Sauran mambobin kwamitin sun hada da gwamnan jihar Akwa Ibom, da na Ogun, Borno, Plateau da kuma Jigawa.

 

Gwamnonin sunce basa adawa da sabon tsarin na sauya fasalin naira saidai akwai bukatar a sake duba wasu tsare-tsare da a cikinsa.

 

Gwamnonin sun bayyana kudurin yin aiki kafada-da-kafada da babban bankin kasa CBN don inganta wuraren da ke bukatar fadakarwa game da sabon tsarin.

Latest stories

Related stories