Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN ya fara cin tarar bankuna naira miliyan 1 a kullum kan...

CBN ya fara cin tarar bankuna naira miliyan 1 a kullum kan kin saka sabbin kudi na naira.

Date:

Babban Bankin Ƙasa, CBN, ya fara daukar matakin ladabtar da bankuna ta hanyar cin tarar su Naira miliyan 1 a kowace rana ga kowane banki da ya ƙi karba da raba sabbin takardun Naira gabanin wa’adin ranar 31 ga watan Janairun 2023.

 

Shugabancin bankin CBN ya bayyana haka ne a jiya Juma’a a yayin wani shirin wayar da kai ga ƴan kasuwa mata a Jihar Osun da aka shirya a kasuwar Ayegbaju, domin fadakar da su kan sabbin takardun Naira na N200, N500 da N1000 da aka sauya wa fasali.

 

Da ya ke jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan hada-hadar kuɗi na CBN, Adeleke Adelokun ya bayyana cewa CBN ya buga isassun sabbin takardun kudi na naira, amma bankunan sun ki karba.

 

A halin da ake ciki, Kwanturola na CBN, reshen Osogbo, Madojemu Daphne wanda ya samu wakilcin Adebayo Omosolape ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun ɓoye tsofaffin takardun naira har na naira tiriliyan 2.7.

Latest stories

Related stories