Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbin da ya sa Najaatu Bala ta yi murabus daga kwamitin yakin...

Abin da ya sa Najaatu Bala ta yi murabus daga kwamitin yakin neman zaben Tinubu na APC

Date:

A makon da muke shirin bankwana da shi ne Hajiya Najatu Muhammad, ta yi murabus daga mukaminta tare da ficewa daga APC.

 

Hajiya Najatu wadda itace Daraktar kungiyar fararen hula na kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, tuni ta sanar da yin murabus daga mukamin nata.

 

Wannan na dauke cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 19 ga watan Junairu, 2023, wadda Najatu ta aike zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, inda ta bayyana ficewarta a hukumance.

 

Naja’atu Muhammad, ta ce kalubalen da Najeriya ke fuskanta na bukatar ta ci gaba da fafutukar ganin an samar da kasa mai inganci ya sanya ta fice daga APC.

 

Cikin wasikar da ta fitar ta bayyana cewa “Ina sanar da ku game da yin murabus dina a matsayin Darakta Kamfen din shugaban kasa na APC,’

 

“Duk da haka, da dama daga cikin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a fagen siyasa da dimokuradiyyar kasar nan, sun sa ba zan iya ci gaba da shiga harkokin siyasar jam’iyya APC ba,’ a cewar ta.

 

Naja’atu Muhammad dai ta fice daga jam’iyyar yayin da ake shirin shiga zaben shugaban kasa a wata mai kamawa wato ranar 25 ga Fabrairun 2023.

Latest stories

Related stories