Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSiyasaInec Ta Shirya Tunkarar Matsalar Sayen Kuri'u-Farfesa Mahmood

Inec Ta Shirya Tunkarar Matsalar Sayen Kuri’u-Farfesa Mahmood

Date:

Abdurrashid Hussain

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta dauki kwararan matakai domin magance matsalar sayen kuri’u a zaben badi.

 

Shugaban hukumar farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, a wani taron da ya hada masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Abuja.

 

Ya ce daga cikin matakan da hukumar ta dauka sun hada da samar da hukumar hukunta masu aikata laifukan zabe da cigaba da ilimantar da jama’a illar sayen kuri’a.

 

Har ila yau, INEC na aiki da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC, sai kuma sake fasalin rumfunan zabe.

 

Ya ce muddun hukumar ta inganta hanyoyin zabe to kuwa za’a samu sauki wajen dakile aikata magudi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories